Hukuncin da Za a Fara yi wa Masu Fyade
Gwamnatin Jihar Sokoto ta tsaurara hukuncin da doka ta tanada ga masu fyade da cin zarafin mata a jihar.
A karkashin dokar da aka aiwatar, an tanadi hukuncin daurin rai da rai ba tare da zabin tara ba ga wanda aka samu ya aikata fyade.
Gwamnatin jihar Sokoto ta sanar da hakan ne yayin kaddamar da cibiyar sauraron korafin fyade da cin zarafin mata.
Gwamnatin Jihar Sokoto ta zartar da sabuwar doka da ta tanadi daurin rai da rai da wadanda aka samu da laifin fyade da wasu laifuka masu alaka da fyaden.
Read Also:
Gwamna Aminu Tambuwal ne ya bayyana hakan a jiya (Alhamis) a wurin taron kaddamar da cibiyar sauraron korafe-korafen fyade da cin zarafin mata da aka saka wa sunan diyar shahararren malami, Sheikh Usman Bin Fodiyo, Nana Khadija.
A cewar gwamnan, jihar ta sake jadadada dokar Penal Code ta shekarar 2019 wacce tuni majalisa ta amince da ita kuma ya saka hannu a kai.
Ya yi bayanin cewa akwai wani sashi na dokar ta ya tanadi hukuncin daurin rai da rai ga wadanda ke cin zarafin mutane saboda jinsinsu.
“A baya, a kan yanke hukunci mai sassauci kamar shekaru biyu. Amma yanzu, daurin rai da rai ne da tara da ta fara daga naira 50,000 zuwa miliyan daya,” a cewar gwamnan da kwamishinan shari’a na jihar, Sulaiman Usman ya wakilta.
Gwamnan ya ce babu zabin tara ga wanda ya aikata fyade kuma an kara wa’adin zaman gidan gyaran halin. Ya sake jadadda niyyar gwamnatin jihar na yin hadin gwiwa da duk wata cibiya ko kungiya don kawo karshen cin zarafin mata da ake yi a jihar.