Rashin Imani: Dalilin da Yasa Wani Soja ya Zane Budurwa

Ya dakeni kamar bakuwar karya, cewar wata budurwa a kan wani sojan Najeriya.

A cewarta, tana cikin tafiyarta, ko kallonsu bata yi ba, sai ta ji bulala a gadon bayanta.

Ga mamakinta, sai sojan yace wai ta wucesu bata gaishesu bane shiyasa ya zaneta Wata budurwa mai suna Olaide Oluwo, tana bukatar a yi mata adalci bayan wani sojan Najeriya da ke Sangotedo, jihar Legas ya ci zarafinta a ranar Laraba, 25 ga watan Nuwamba.

Kamar yadda ta wallafa bidiyonta a kafar sada zumuntar zamani, wanda tace ya ci zarafinta ne saboda ba ta gaishesu ba.

“Wannan al’amarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yamma. Ban yi musu komai ba.

Ko kallonsu ban yi ba, sai ga daya daga cikinsu da bulala, ya fara bugu na kamar jaka! Ina cikin tafiya ya zage ni kuma ya bi ni yana duka da bulala.

“Da mutane su ka tambayesa dalilin yin hakan, sai yace na wuce su ba tare da na gaishesu ba, shiyasa ya dauki wannan hukuncin a kaina,” a cewarta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here