Za Muyi Duk Wani Kokari Akan Rashin Lafiyar Josphe Wayas- Gwamnatin Cross-River  

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Joseph Wayas, yana kwance a asibiti rai a hannun Allah a Landan.

Sanata Joseph Wayas ya shugabanci majalisar dattawar Najeriya a jamhuriya ta biyu daga 1979 zuwa 1983.

Gwamnatin Jihar Cross Rivers ce ta dauki dawainiyar yi masa magani kamar yadda gwamnan jihar Ben Ayade ya umurta.

Tsohon shugaban majalisar dattawar Najeriya, Sanata Joseph Wayas, yana wata asibiti a birnin Landan sakamakon rashin lafiya da ya ke fama da ita kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wayas shine shugaban majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu daga shekarar 1979 zuwa 1983 a lokacin da marigayi Alhaji Shehu Shagari ke shugaban kasa.

An dade ba a ga Wayas ba a cikin mutane a shekarun baya bayan nan.

Gwamna Ben Ayade na Jihar Cross River wanda ya tabbatar da rashin lafiyar tsohon shugaban majalisar ya ce jihar zata dauki nauyin yi wa dattijon kasar magani.

Ayade ya umurci kwamishinan lafiya na jihar Cross River, Dakta Betta Edu da tawagarta su tafi da shi Landan nan take kuma su cigaba da sa ido kan kulawar da ake bashi.

Gwamnan cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Christian Ita, hadiminsa na bangaren watsa labarai ya ce: “Jihar ba zata yi kasa a gwiwa ba wurin kashe kudi don ganin an samarwa tsohon shugaban majalisar lafiya.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here