Taraba: Anyi Garkuwa da Wani ‘Dan birnin Sin Tare da Direbansa

Ana zargin masu garkuwa da mutane sun sace wani Basinne a jihar Taraba.

Miyagu sun dauke wani Ma’aikacin kasar Sin da direbansa a hanyar Wukari.

Wadannan ‘Yan bindiga ba su bukaci karbar kudin fansa ba har zuwa yanzu.

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin cewa masu garkuwa da mutane ne, sun sace wani kwararren ma’aikaci da ke aiki a Najeriya daga kasar Sin.

Daily Trust ta ce wadannan miyagu sun sace mutumin kasar Sin din ne tare da wani direbansa a kan hanyar Donga zuwa garin Wukari, jihar Taraba.

Kamar yadda jaridar ta bayyana, ‘yan bindigan sun tare titin ne, daga nan suka dauke Basinen da direbansa ba tare da jami’an tsaro sun yi komai ba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wadannan Bayin Allah suna cikin mota kirar Jeep lokacin da wadanda ake zargin masu garkuwan suka kama su.

‘Yan bindigan sun tuntubi wurin aikin mutumin a garin Donga, suka sanar dasu cewa sun tsare ma’aikacinsu tare da kuma wanda yake tuka motarsa.

Miyagun sun tabbatar da cewa mutanen biyu suna nan garau cikin koshin lafiya, amma har zuwa yanzu haka, ba su bukaci a biya kudin fansa ba tukuna.

Kakakin ‘yan sandan jihar Taraba, DSP David Misal ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma bai iya cewa komai ba a lokacin da ‘yan jarida suka tuntube shi.

Jama’a sun kaurace wa titunan Donga da Takum a yankin Kudancin jihar Taraba, a dalilin ta’adin da ‘yan bindiga da kuma masu garkuwa da mutane suke yi.

A kwanakin baya ne ma aka samu mutane suna bin wadannan hanyoyi, bayan abubuwa sun lafa.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here