ɓoye Sabbin Kuɗi: ICPC ta Kama Manajojin Banki Biyu
Hukumar yaƙi da laifukan cin hanci da rashawa a Najeriya, ICPC, ta kama manajan ayyuka na reshen bankin FCMB a Jihar Osun saboda zargin ɓoye sababbin takardun naira.
ICPC ta ce ta gano an zuba kuɗi a cikin na’urorin ATM na bankin amma a ɗaɗɗaure ta yadda ba za su iya fita ba idan mutane suka je cira, inda ta yi gargaɗi da a gyara.
Read Also:
“Sai dai da tawagar ta sake kai ziyarar duba a rana ta biyu, sai ta tarar ɗaya daga cikin ATM ɗin na ɗauke da ɗaurarrun kuɗin,” a cewar sanarwar da ICPC ta wallafa a shafukan zumunta.
Bisa wannan dalilin ne kuma jami’an hukumar suka tafi da manajan mai kula da ayyuka, wanda ba ta bayyana sunansa ba, na reshehn bankin na FCMB.
Haka nan, ICPC ta kama wata manajar bankin a Abuja “saboda ƙin saka kuɗi a ATM da gangan ko kuma sabo da mugunta duk da cewa akwai kuɗin,” in ji hukumar.
Jami’an tsaro da suka haɗa da na ‘yan sanda da EFCC na ci gaba da bin sawun bankuna da ɗaiɗaikun mutane don yaƙi da masu ɓoyewa da sayarwa da kuma yaɗa takardun jabu na sababbin kuɗin.