IGP: Ya Umarci ‘Yan Sandan Najeriya da Su Gaggauta Komawa Wuraren Aikinku
Sifeta janar na ‘yan sanda, ya umarci ‘yan sanda da su koma bakin aikinsu.
Ya ce kada su kuskura su bar bata-gari da ‘yan ta’adda su cigaba da yin yadda suka ga dama.
Ya musanta labarin masu zanga-zangar EndSARS da aka ce ‘yan sanda sun kai musu farmaki Adamu ya yi wa ‘yan sanda jawabi a hedkwatar Edo da ke GRA Benin, lokacin da yake ba wa ‘yan sanda kwarin guiwa a kan konannun ofisoshin su da aka kona a jihar Edo.
Read Also:
IGP din wanda ya samu rakon mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, mataimakin sifeta janar na ‘yan sanda, Shola David da kwamishinan ‘yan sanda, Babatundu Kokumo, The Nation ta ruwaito.
A cewarsa: “Farmakin da aka kai wa ‘yan sanda da ofisoshinsu an yi ne don a wulakantasu, kuma a nuna musu cewa mutane ba sa mara musu baya.
“‘Yan sanda jami’ai ne na musamman saboda an horar da su musamman don taimakon al’umma. “Shiyasa duk da harin da aka kai mu ku, kuka share su, kuma ku ka tsaya kai-da-fata wurin taimakonsu.
“Ina kara ba ku kwarin guiwa, kada ku sare, ku tabbatar kun cigaba da tabbatar da tsaro a wurare daban-daban.”