ASUU: A Shirye Muke mu Koma Bakin Aikin Mu

ASUU ta ce za ta iya koma wa bakin aiki da zarar an biya su hakkokinsu.

Wani shugaban kungiyar Malaman, Ade Adejumo ya bayyana haka dazu.

Farfesan ya fadi abubuwan da su ka sa dole ASUU ta tafi dogon yajin aiki Bayan kimanin watanni bakwai da rufe jami’o’in gwamnati a Najeriya, Daily Trust ta rahoto kungiyar ASUU ta na maganar bude makarantu.

Malaman jami’a sun bayyana shirinsu na komawa aiki muddin gwamnatin tarayya ta biya su bashin albashin wata da watanni da aka hana su.

Shugaban kungiyar ASUU na reshen Ibadan, Farfesa Ade Adejumo ya bayyana shirinsu na bude makarantu a lokacin da ya yi hira da ‘yan jarida.

Kamar yadda rahotanni su ka shaida, Ade Adejumo ya zanta da manema labarai ne a ranar Laraba a babban dakin taron sashen fasaha na jami’ar Ibadan.

Farfesa Adejumo ya ce duk da su na zama da gwamnatin tarayya domin a samu mafita, an hana malaman jami’a albashin watanni da alawus dinsu.

Sauran jagororin ASUU da su ka halarci taron sun hada da Moyosore Ajao, Ayo Akinwole, Femi Abanikanda, Biodun Olaniran da kuma Dauda Adesola. Wakilan na ASUU sun fito ne daga jamo’in Unilorin, UI, Unisoun, LAUTECH da KWASU.

Farfesa Moyo Ajao shi ne ya wakilci Farfesa Ade Adejumo a zaman na yau. Ajao ya ce dole ce ta sa kungiyar ASUU ta tafi yajin-aiki a watan Maris. Ya ce: “ASUU ta na yajin-aiki ne domin dawo da martabar jami’o’i.

ASUU ta na yajin-aiki ne saboda ‘ya ‘yanta da ke karbar mafi karancin albashi.”

Malaman Jami’a da ke yajin aiki a Najeriya sun dura kan Ministan ilmin, sun yi masa raddi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here