Tsohon Firaministan Pakistan, Imran Khan ya Shiga Hannu
An kama tsohon firaministan Pakistan, Imran Khan a wajen babbar Kotu da ke birnin Islamabad.
Mista Khan na hanyar halartar zaman kotu, inda ake tuhumarsa da rashawa, wanda ya yi zargin cewa bi-ta-da-kullin siyasa ce kawai.
Read Also:
Hotunan da aka wallafa sun nuna yadda jami’ai sanye da kakin ma’aikatan tsaro, suka kama Mista Khan lokacin da ya shiga harabar kotun, sannan daga bisani suka tafi da shi.
A watan Afrilun bara ne, aka hambarar da shi daga kan mulki, kuma tun daga wannan lokaci yake gangamin ganin an gudanar da zaɓe a kan lokaci.
A bana, ake sa ran gudanar da babban zaɓe na kasar.