An Tsaurara Matakan Tsaro a Babban Birnin Rasha

 

An tsaurara matakan tsaro a Moscow babban birnin Rasha, a yayin da ake shirin faretin bikin ranar nasara wadda aka fi sani da Victory Day.

Ana gudanar da bikin ne domin tunawa da galaba a kan sojojin Nazi a Yakin Duniya na Biyu.

Shugaba Putin ne zai jagoranci faretin na soji a yayin da ake cikin rudani a wannan shekarar, sakamakon yakin Rasha da Ukraine.

A makon da ya gabata an kai hari kan fadar Kremlin.

An dai soke bikin tunawa da ranar nasara ta victory day din a biranen Rasha da dama.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here