Kotun Kolin Indiya ta Bawa Mata Damar Zubar da Ciki

 

Kotun Kolin Indiya ta ce dukkan mata ciki har da marasa aure suna iya zubar da ciki ko da juna biyun ya haura mako 24.

Hukuncin kotun ya zo ne baya wani roko da aka gabatar don neman a fayyace dokar zubar da ciki da aka yi wa gyara wadda ta lissafa rukunoni da yawa amma ba ta ambaci matan da ba su da aure ba.

Kotun ta ce dukkan mata, ba tare da la’akari da matsayin aure ba, na da ikon zubar da ciki bisa doka kuma ta hanya mai aminci.

Ta ce tsame matan da ba su aure bayan wata alaka tsakanin namiji da mace cikin yarda da juna “keta tsarin mulki” ne.

Zub da ciki halas ne a Indiya tun cikin 1971, amma tsawon shekaru hukumomi sun tsaurara dokoki game da wane ne zai iya baras da juna biyu saboda miliyoyin ‘yan tayin mata da ake zubarwa, lamarin da ya janyo gagarumin bambanci tsakanin adadin jinsin maza da na mata a kasar.

A al’adance, Indiyawa sun fi son haifar ‘ya’ya maza a kan ‘ya’ya mata.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here