Najeriya za ta Ci gaba da Kasancewa Dunkulalliyar Kasa Guda – IBB

 

Tsohon shugaba kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya) ya shawarci al’ummar kasar su zama masu kwarin gwiwa da kyakkyawan fata duk da matsalolin da Najeriya take ciki.

Najeriya in ji shi, za ta ci gaba da kasancewa dunkulalliyar kasa guda.

Janar Babangida na wannan jawabi lokacin zantawa da manema labarai a Minna kafin bikin cikar Najeriya shekara 62 da samun ‘yanci, kamar yadda Gidan Talbijin na Channels ya ruwaito.

Don ganin haka, Janar Babangida ya ce akwai bukatar kowa ya kara himma.

Ya yaba wa kokarin gwamnatoci daban-daban a Najeriya wajen ganin kasar ta ci gaba da zama dunkulalliya, ya kuma yi kira don samun karin nasarori.

Ya ce burinsa shi ne ya ga Najeriya ta zama kasa mai karfi da yalwar arziki da hadin kai ta yadda zaman lafiya zai zarce komai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here