Indonesia: An Haramta Siyar da Kayayyakin Faransa

Shaguna a kasar Indonesia sun dakatar da siyar da kayayyakin kasar Faransa.

Hakan mataki ne da suka dauka domin yin Allah-wadai da batancin da aka yi wa Annabi Muhammad a Faransa.

Sun ce sun gwammaci yin asarar dukiya a kan batancin da aka yi wa fiyayyen halitta Rahotanni sun kawo cewa an haramta siyar da kayayyakin kasar Faransa a kasar Indonesia, hakan mataki ne na nuna bacin rai a kan kare zanen barkwanci da wata mujjalla ta yi kan Annabi Muhammadu (SAW) Tuni dai wasu shagunan makarantar kwana a gabashiun ava da Yammacin Kalimantan mai suna “Basmalah Shop” ta yi umurnin cire duk wasu kayayyaki da yake na kasar Faransa a shagon, TRT Hausa ta ruwaito.

Mataimakin shugaban shagon Basmalah Shop, Ahmad Edy Ami, ya bayyana cewa, “Mun dauki wannan matakin ne domin kalubalantar yunkurin tsokana da wulakanta Musulmi da Faransa ke yi, duk da hakan zai sanya mu rasa wasu kudade mun gwamacewa muyi hada kai da Musulmi domin yin Alla-wadai ga batancin da ake yi musu” Shugaban Shura a yankin Kudancin Sulawesi, Muhammed Hiday Hanis, ya bayyana cewa shagunan yankin duk sun dakatar da siyar da kayayyakin Faransa a shagunansu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here