Hukumar INEC ta Janye Daukaka ƙarar da ta yi Kan Hukuncin Zaben Gwamnan Kano

 

Hukumar zaɓe ta ƙasa ba za ta cigaba da neman daukaka ƙara ba kan hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan Kano ta yanke.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun shugaban sashin shari’a na hukumar a ranar Juma’a 6 ga watan Oktoba.

A cikin takardar dai an tabbatar da cewa umarnin janye ƙarar ya fito ne daga hedikwatar hukumar da ke Abuja.

Jihar Kano – Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta janye ƙarar da ta ɗaukaka kan hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke.

An tabbatar da hakan ne a wata wasiƙa mai dauke da sa hannun Suleiman Alkali, shugaban sashin shari’a na hukumar a Kano, a ranar Juma’a, 6 ga watan Oktoba.

Kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto, wasiƙar na cewa:

“Hedikwatar hukumar INEC ta umurce ni da cewa a hukumance ba ta da wani dalili na ɗaukaka ƙara kan wannan hukunci.”

“Saboda haka, sashen hukumar da ke kula da harkokin shari’a da kuma kwamishinan hukumar na ƙasa mai kula da shiyyar Kano sun ba da umarnin a janye ƙarar, kuma a mika duk wani tsari na duk ɗaukaka ƙara ga ofishin Kano.”

INEC ta ɗaukaka ƙara Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta shigar da ƙara kan hukuncin kotun, inda ta ce kotun sauraron ƙararrakin zabe ta yi kuskure a cikin doka inda ta ayyana ɗan takarar masu shigar da ƙara, wanda ba ya cikin ƙarar a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Idan za’a tuna a ranar Litinin 29 ga watan Mayu ne aka rantsar da gwamna Yusuf bayan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jihar Kano, kuma hukumar zaɓe ta miƙa masa takardar shaidar cin zabe.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com