Shin Ko Ramuwar Gayya ce ta sa ‘Yan Bindiga Suka Sace ɗaliban FUDMA ?

 

Mataimakin shugaban jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma (FUDMA) a jihar Katsina, ya bayyana dalilin sace ɗalibai a jami’ar.

Armaya’u Bichi ya bayyana cewa ƴan bindigan da suka sace su ramuwar gayya suka zo yi kan harin da jami’an tsaro suka kai musu.

Bichi ya ƙara da cewa jami’an tsaro na bakin ƙoƙarinsu domin ganin cewa ɗaliban sun shaƙi iskar ƴanci.

Jihar Katsina – Yan ta’addan da suka sace ɗalibai biyar na jami’ar tarayya da ke Dutsinma a jihar Katsina, ramuwar gayya suka je yi.

Mataimakin shugaban jami’ar, Armaya’u Bichi ya bayyana cewa ƴan bindigan sun sace ɗaliban ne domin ramuwar gayya kan harin da jami’an tsaro suka kai kan wasu ƴan uwan mambobinsu.

Premium Times ta rahoto cewa Farfesa Bichi, yayin wata tattaunawa da DW Hausa a yammacin ranar Juma’a, 6 ga watan Oktoba, ya ce masu garkuwar sun bayyana dalilin yin garkuwa da daliban a wata tattaunawa domin ganin an sako su.

An sace ɗaliban ne a ranar Larabar da ta gabata a lokacin da ƴan ta’addan suka kai farmaki gidansu da ke unguwar Mariamoh Ajiri a cikin garin Dutsin Ma.

Ko ƴan bindigan sun buƙaci kuɗin fansa?

Farfesa Bichi, bai bayyana ko ƴan ta’addan sun buƙaci a biya su kuɗin fansa domin a sako ɗaliban ba.

A kalamansa:

“Ana ci gaba da tattaunawa da su (ƴan ta’adda). Hukumomin tsaro suna yin iya bakin ƙoƙarinsu (don kuɓutar da ɗaliban).Su (ƴan ta’addan) sun yi magana kuma sun ce ramuwar gayya ce ta kai wa iyayensu hari a ƙaramar hukumar Batsari.

An ƙona gidaje na iyayensu tare da kwashe shanunsu da kuma hatsi.” “Sun so su rama harin da aka kai a Batsari amma wani shugaban ƙungiyar ƴan ta’adda bai goyi bayansu ba inda ya hana su, shi ne sai suka zo Dutsin Ma domin ɗaukar fansa.”

“Amma su (ƴan ta’adda) an gaya musu gaskiya cewa mutanen Dutsinma da daliban ba su yi musu laifi ba don haka su sako daliban da aka sace. Mun yi imanin cewa da yardar Allah za su sake su.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com