2023: Hukumar INEC ta Soke Rajistar Mutane 1,126,359 a Najeriya
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta sanar cewa ta soke rajistar wasu mutum 1,126,359 cikin sabuwar rajistar mutum 2,523,458 da ta yi tsakanin 28 ga watan Yuni zuwa 14 ga watan Janairu, 2022.
Read Also:
Babban kwamishinan hukumar ta INEC Festus Okoye ne ya sanar da haka cikin wani sakon Tiwita da hukumar ta wallafa a shafinta a ranar Litinin a Abuja.
Ya ce “INEC ta gano cewa wasu mutanen ba su yi rajista daidai da tsarin doka ya tanadar ba, saboda haka ne muka soke rajistar tasu baki daya.”
INEC ta kuma ce mutum 1,397,099 da suka yi sabuwar rajista ne kawai za a saka sunayensu cikin kundin wadanda za su iya zakda kuri’arsu a babban zabe da ke tafe a shekara mai zuwa.