Mun Soke Rajistar Mutane Miliyan 2.7 Wadanda Suka yi Sau Biyu – INEC
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeria, INEC, ta ce ta soke rajistar mutum miliyan 2.7 waɗanda aka gano sun yi rajistar fiye da sau ɗaya.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya bayyana haka a wani taron tataunawa kan mulkin demokraɗiyya da ya gudana a birnin Washington na ƙasar Amurka.
Read Also:
A cikin bayanin da ya yi, shugaban hukumar ta INEC, ya ce nan da watan Nuwamba mutane za su iya karɓar sabbin katunan zaɓen nasu.
Ya ce yanzu haka ma an kammala haɗa kashi 50% na katunan zaɓen.
Sai dai a cewar sa wata babbar matsalar da ke damun hukumar ita ce rashin tsaro a faɗin Najeriya.
Ya ce hukumar tana sanya ido kan musamman abubuwan da ke faruwa a arewa-maso-yammaci da kuma kudu-maso-gabacin kasar.
Sai dai a cewarsa hukumar ta INEC ta gana da shugabanni a ɓangaren tsaro na ƙasar waɗanda suka tabbatar mata cewar lamurra za su gyaru kafin lokacin zaɓen.