INEC: Ta Yanke Shawara Aka Ranar Zaben Maye Gurbi
INEC, hukumar zabe ta kasa, ta ce ta daga zabukan maye gurbi 15 da ta yi niyyar gudanarwa a cikin watan Oktoba saboda dalilan tsaro.
Barista Festus Okoye, kwamishinan yada labarai a INEC, ya ce mahukunta a hukumar sun gudanar da muhimmin taro ranar Juma’a a Abuja.
Bayan kammala taron, INEC ta yanke shawarar gudanar da zabukan maye gurbin a ranar Asabar, 5 ga watan Disamba Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta tsayar da 5 ga watan Disamba, 2020, a matsayin ranar gudanar da zabukan maye gurbi guda 15 a jihohi 11.
Barista Festus Okoye, kwamishinan yada labarai da ilimintar da masu zabe, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.
Read Also:
A cikin sanarwar, Barista Okoye ya ce; “mahukunta INEC sun gana a yau Juma’a, 13 ga watan Nuwamba, 2020, domin tattaunawa a kan ayyukan hukumar kamar yadda aka saba duk bayan watanni uku.
“Kazalika, an tattauna a kan zabukan maye gurbi 15 da Za a yi a jihohi 11.
“Idan jama’a basu manta ba, a baya hukumar INEC ta tsayar da ranar Asabar, 13 ga watan Oktoba, 2020, domin gudanar da zabukan maye gurbin, amma daga baya aka daga saboda dalilan tsaro.
“Bayan tattaunawar INEC da dukkan masu ruwa da tsaki a harkar zabe, hukumar ta yanke tsayar da ranar Asabar, 5 ga watan Disamba, domin gudanar da zabukan.”
INEC ta bayyana cewa ta yaba da hadin kai da fahimtar da jam’iyyun siyasa da jami’an tsaro suka nuna dangane da batun daga zaben.
“Mu na kira ga ma su zabe da sauran ma su ruwa da tsaki a harkar zabe da su bawa INEC hadin kai domin samun damar sauke nauyin da ke wuyanta na gudanar da sahihin zabe da kowa zai gamsu da sakamakonsa,” kamar yadda INEC ta fada a cikin sannarwar da ta fitar.