Sarkin Saudiyya ya Kira Buhari ta Wayar Salula

 

Sarki Salman bin Abdulaziz na kasar Saudiyya ya kira Shugaba Muhammadu Buhari ta wayar tarho.

Shugabannin biyu sun tattauna kan batutuwan da suka shafe kawancen diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Ko a watan Agusta, Sarki Salman ya kira Shugaba Buhari ta waya inda nan ma suka tattauna kan farashin man fetur na duniya .

Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz Al Saud ya kira Shuguba Muhammadu Buhari na Najeriya a wayar tarho, a ranar Alhamis kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyya ya ruwaito.

Shugabanin biyun sun tattauna batutuwa ne masu alaka da kawancen diflomasiyya da ke tsakaninsu da hanyoyin da za a bi don inganta yarjejeniyar da ke tsakanin kasashen biyu a cewar Saudi Gazette.

Wannan shine karo na biyu da sarkin na Saudiyya ke kiran Buhari ta waya.

A baya cikin watan Agusta, Sarki Salman ya kira don tattaunawa kan hanyoyin da za a daidaita farashin man fetur a kasuwannin duniya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here