Mohammed Salah: Shahrarren Dan Kwallon ya Kamu da Cutar Coronavirus

Shahrarren dan kwallon kasar Masar kuma mai bugawa kungiyar kwallon Liverpool, Mohamed Salah ya kamu da muguwar cutar Coronavirus.

Kungiyar kwallon kasar Masar ce ta sanar da hakan a shafinta na yanar gizo ranar Juma’a, Punch ta gano.

Ya kamu da cutar ne yayinda ya tafi wasa kuma zai killace kansa.
“Gwajin cutar Koronan da muka gudanar kan yan kwallonmu ya nuna cewa dan wasa, Mohamed Salah, tauraron Liverpool, ya kamu da cutar,” jawabin yace.

“Babu wasu alamun kamuwa da cutar tattare da shi, kuma sauran yan kwallon basu kamu ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here