Kungiyar IPOB na Samun Goyan Bayan ‘Yan Kasashen Waje da Ake Biyansu Albashi Mai Tsoka- Shugaba Buhari

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da ayyukan kungiyar nan mai neman ballewa ta Indigenous People of Biafra.

Shugaban Najeriyan ya bayyana dalilin da ya sa ayyukan haramtaciyyar kungiyar ba shi da amfani.

Buhari ya nuna kwarin gwiwar cewa Najeriya za ta ci gaba idan ‘yan kasa ba su yarda su zama wakilan rabuwa ba.

Abuja – Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya yi zargin cewa haramtaciyyar kungiyar nan ta Indigenous People of Biafra (IPOB) na samun goyon bayan wasu ‘yan kasashen waje da ake biyansu albashi mai tsoka.

Buhari ya yi wannan zargin ne a ranar Litinin, 30 ga watan Agusta, a cikin wata sanarwa da Garba Shehu, babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai ya fitar.

Ya yi zargin cewa kungiyar tana aikata ayyukan ta’addanci ne domin satar kudi.

Buhari ya bayyana cewa IPOB ba gwagwarmayar neman ‘yanci take yi ba yayin da suke kai hari kan ofisoshin ‘yan sanda da kadarori.

Shugaban kasar ya yi watsi da hasashen cewa kungiyar na kare hakkin Kiristoci ne.

Ya ce:

”IPOB ba Kiristoci take karewa ba – kamar yadda masu fafutukarsu na kasashen waje da ake biya makudan kudade suke da’awa – a yayin da kusan dukka ‘yan asalin jahohin da suke addaba suka kasance Kiristoci ne.”

Shugaban kasar ya bayyana cewa masu fakewa a bayan ‘yan kungiyar ne suka yaudare su. Ya ce wasu kafofin watsa labarai na kasashen waje da ‘yan siyasa sun yarda da labarin karyar na cewa IPOB tana wakiltar muradun Kiristoci ne.

Shugaban kasar ya bukaci ‘yan Najeriya da su hada kai su yi adawa da wadanda ke kokarin haddasa rarrabuwar kawuna a kasar saboda son rai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here