Corona: Karin Mutane 460 Sun Kamu da Cutar a Najeriya

 

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 460 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a ranar Litinin.

Hukumar ta ce akasarin waɗanda suka kamu a jahar Rivers suke inda aka samu karin mutum 164 dauke da cutar, yayin da a Lagos aka samu mutane 139 da gwajin da aka yi musu ya tabbatar da cewa sun kamu da cutar.

Ga jerin jahohin da aka samu bullar cutar ranar Litinin:

Rivers-164

Lagos-139

Edo-64

FCT-37

Bayelsa-20

Oy0-14

Plateau-7

Ogun-6

Anambra–4

Benue-4

Enugu-2

Cross River-1

Kaduna-1

A jimillance adadin mutanen da suka kamu a faɗin ƙasar sun kai 191 805 sai dai 178,492 sun warke.

Akwai kuma mutum 2,455 da suka mutu.

A baya-bayan nan ne aka samu ɓullar sabon nau’in cutar corona da ake kira Delta a Najeriya, wanda masana ke cewa yana da saurin yaɗuwa matuƙa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here