Iyaye Sun yi Watsi da Tayin Diyyar Dala Dubu 20,000 na Yaransu da Suka Mutu Sakamakon Shan Maganin Tari
Iyayen yara 70 da suka mutu sakamakon cutar koda, da ake zargin sun kamu da ita saboda shan wani maganin tari da aka yi a kasar Indiya, sun yi watsi da tayin diyyar dala 20,000 da gwamnati ta yi musu.
Ma’aikatar kula da cigaban al’umma ta kasar ce ta yi tayin bayar da diyyar dala 20,000 ga iyayen yaran domin su raba tsakaninsu.
Shugaban kungiyar iyayen yaran Ebrima Sanyang ya ce karbar tamkar kudin ‘cin mutunci’ ne ga yaran da suka mutu.
Ya ce karbar kudin na nuna cewa ba da gaske suke nema wa yaran adalaci ba.
Read Also:
Iyayen na bukatar hukumar da ke kula da magungunta kasar da ta janje kalaman da ta yi tunda farko, inda ta ce yaran sun mutu ne sakamakon ambaliyar ruwa, ba daga shan maganin tarin ba.
Suna kuma bukatar a hana hukumar kula da magungunan, gudanar da binciken da shugaban kasar ya yi kira da a gudanar.
A watan Oktoba Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadi ga kasashen duniya cewa akwai wasu nau’in magungunan tari hudu da ke kawo lalacewar koda, bayan da aka samu rahotonnin da ke cewa an samu yaran Gambiya da matsalar cutar kodar bayan shan maganin.
To sai dai kamfanin da ke samar da magungunan mai suna ‘Maiden Pharmaceuticals’ ya ce yana bin matakan ingancin magunguna da duniya ta amince da su.