Duk Mai ƙaunar Atiku Maƙiyin Jihar Benuwai ne – Gwamna Ortom

 

Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, yace ba zai mara wa ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar baya ba a 2023.

Gwamnan, wanda ya fito daga arewacin Najeriya yace ya gwammaci ya mutu da ya goyi bayan Bafullatani ya zama shugaban ƙasa.

Ortom na ɗaya daga cikin tawagar gwamnoni 5 da suka ware kansu a PDP kuma suka nemi Ayu ya yi murabus.

Benue – Gwamnan Jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya aike da kakkausan sako ga Atiku Abubakar, mai neman shugaban kasa a inuwar PDP, ya faɗa masa ba zai goyi bayan takararsa ba.

Jarisar The Nation ta rahoto Gwamnna Ortom na faɗa wa Atiku cewa can ta matse masa, amma ba zai mara masa baya ba yayin da Fulani ke kashe mutanensa a Benuwai.

Ortom ya yi wannan furucin ne ranar Lahadi da daddare yayin da ya karɓi bakuncin gwamnonin G-5 da suka haɗa da, Nyesom Wike na Ribas, Okezie Ikpeazu na Abiya; Seyi Makinde na Oyo da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.

Gwamnan ya koka da kisan da aka yi wa mutane 18 a ƙaramar hukumar da ya fito a makon da ya gabata, inda yace:

“Can ta matse wa Atiku da duk masu goyon bayansa, ku je ku gaya masa shin yana son na zama bawan Fulani ne? Gara na mutu, duk mai ƙaunar Atiku maƙiyin jihar Benuwai ne.” “Ana ta kashe mutane na amma ku ce in yi shiru.

Wa’adin mulkina zai kare a watan Mayu, daga nan zaku iya mun duk abinda kuka ga dama idan kuna tunanin kuna da mulki, na riga na rubuta wasiyyata.”

“Lokacin da na baiwa matata wasiyyata, shafe dare ta yi tana kuka. Idan na mutu a 62 da yawan sa’annina sun riga ni tafiya. Idan yanzun na mutu na cimma nasara amma kowa ya sani na mutu ne a kokarin kare rayuwar mutane na.”

– Samuel Ortom.

Ba zan taba goyon bayan Bafillatani ya zama shugaban kasa ba – Ortom Bugu da ƙari, Gwamna Ortom.yace ba zai taɓa tallafa wa Fulani da ɗare kujerar shugaban ƙasa ba a Najeriya.”

“Ba zan taɓa goyon bayan Bafillatani ya zama shugaban ƙasa ba, idan akwai wani mutum da ke bukatar aiki da ni da tabbatar da tsare rayukan mutanena, an shirya aiki da shi.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here