Mawallafin Jarida Daily Nigerian, Jafar Jafar ya Kai Karar Gwamna Ganduje Wajen Sufeto Janar na ‘Yan Sanda
Mawallafin jaridar Daily Nigerian ya kai karar Ganduje wajen Sufeto-Janar na ‘yan sanda.
Ya bayyana cewa, Ganduje na shirin cutar dashi a wasu jawaban da yayi a makon da ya gabata.
Ya roki Sufeto-Janar din da ya zargi gwamna Ganduje matukar wani abu mummuna ya same shi.
Biyo bayan sabuwar barazanar da ake yi wa rayuwarsa, mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, ya kai kara ga Sufeto-Janar na ’yan sanda, Mohammed Adamu, yana cewa a dauki mataki kan Gwamna Abdullahi Ganduje idan wani abu ya same shi.
A watan Oktoba na shekarar 2018, Jaafar ya wallafa wasu faya-fayen bidiyo da ke nuna yadda gwamnan ke sakama daloli a aljihu da ake zaton cin hanci ne daga ‘yan kwangila da ke gudanar da ayyuka daban-daban da gwamnatin jahar ta bayar.
Read Also:
Tuni dai gwamnan ya musanta faya-fayan bidiyon, yana mai bayyana su a matsayin wadanda aka shirya kamar fim. Amma a wata hira da ya yi da Sashin Hausa na BBC a ranar Juma’a, 19 ga Maris, Mista Ganduje ya bayyana cewa gwamnatin jahar na shirin yin maganin wadanda ke bayan bidiyon.
Dangane da sabon barazanan, Mista Jaafar, ta hannun lauyansa, Barista Abdullahi Gumel, ya rubuta wa Sufeto-Janar na ‘yan sanda yana mai nuna masa cewa gwamnan da magoya bayansa suna shirin cutar da mawallafin.
Lauyan ya bayyana cewa Jaafar Jaafar da iyalansa na rayuwa cikin fargaba ba ma a iya jihar Kano ba, har ma a babban birnin tarayya Abuja da sauran sassan kasar.
Ya kuma ce, barazanar baya da rayuwa cikin tsoro bai isa haka ba, “a kwanan nan Mista Ganduje ya nuna cewa shi da magoya bayansa suna kulla makirci ta hanyar “yin maganin” abokin huldarmu.
“Ganduje ya yi wannan bayanin ne a wani shahararren shirin BBC Hausa mai suna “A Fada A Cika” wanda aka gabatar a ranar 19 ga Maris 2021. Ya dage kan cewa ba zai bayyana shirin na su ba duk da wata dama ta fayyace abin da yake nufi.
Lauyan ya zargi gwamna Ganduje da zugi da harzuka magoya bayansa su cutar Mista Jaafar.
Karshe ya bukaci Sufeto-janar na ‘yan sanda da ya kokarta wajen ganin Jaafar Jaafar ya kubuta daga mugun nufin gwamnan.