Kaduna Zuwa Abuja: Mutane 19 Sun Rasa Rayukan su Sanadiyyar Hatsarin Mota

Mutane 19 sun rasu sakamakon hatsarin mota a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Wasu mutanen 34 sun samu raunuka sakamakon hatsarin da ya faru a Kateri.

Kwamishinan tsaro na jahar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da fakuwar hatsarin.

A kalla mutane goma sha tara sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin mota da ya afku a babban titin Kaduna zuwa Abuja.

Hatsarin ya faru ne a ranar Lahadi a kusa da Kateri a babban titin Kaduna zuwa Abuja a cewar sanarwar da kwamishinan tsaro na jahar Kaduna, Samuel Aruwan ya sanar a shafinsa na Facebook.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya yi bayanin cewa hatsarin ya faru ne a yammacin ranar Lahadi da ya ritsa da DAF sakamakon gudu fiye da kima.

Ya yi bayanin cewa tayar motar ta fashe hakan yasa motar ta kwace wa direba sannan ta fada cikin daji.

Mr Aruwan ya ce a kalla mutane 53 ne hatsarin ya ritsa da su; 16 sun mutu nan take sannan wasu uku suka mutu daga baya.

Wasu mutane talatin da hudu sun jikkata, jami’an hukumar kiyayye haddura na kasa, FRSC, sun garzaya da su asibiti domin a yi musu magani.

A cewar wasu da abin ya faru a idonsu, mafi yawancin fasinjojin da ke cikin motar an dako su ne daga Kara, kusa da gidan man fetur, inda wasu za a sauke su a Zaria, yayin da sauran za su sauka a Kano.

Gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufai ya nuna bakin cikinsa kan hatsatrin inda ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu yayin da ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalansu.

Ya kuma yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa. Gwamnan ya kuma shawarci direbobi su rika takatsantsan a dukkan lokuta tare da kauracewa gudu fiye da ka’ida da sauran ganganci a titi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here