Jiga-Jigan PDP Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Kebbi

 

Jam’iyyar PDP ta gamu da sabon koma baya a yunkurinta na kwace mulkin jihar Kebbi daga hannun jam’iyyar APC a zaɓen 2023.

Jigon PDP a ƙaramar hukumar Maiyama, Alhaji Abubakar Kurun Kuku ne ya jagoranci masu sauya sheƙan zuwa APC.

Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar da wasu kwamishinoni da hadiman gwamna sun halarci gangamin karɓan mutanen.

Kebbi – Wani jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ƙaramar hukumar Maiyama, jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Kurun-Kuku, tare da dandazon magoya bayansa sun sauya sheƙa zuwa APC.

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta ruwaito cewa masu sauya sheƙan sun tabbatar da nufin su ne a wurin wani gangami APC da ya gudana a garin Maiyama ranar Talata.

Daily Trust ta ce Shugabannin jam’iyya da cincirindon magoya bayan APC bisa jagorancin shugaban jam’iyya na jiha, Alhaji Muhammad Kana-Zuru, ne suka tarbi masu sauya sheƙar hannu bibbiyu.

Meyasa suka sauya sheƙa?

Da yake sanar da komawarsu APC tare da dandazon mambobi, Alhaji Abubakar Kurun- Kuku, ya ce nagarta da salon tafiyar da mulkin jihar Kebbi na gwamna Atiku Bagudu da yadda ya ɗauki matakai lokacin annobar COVID19 ne suka ja hankalin su zuwa APC.

Ya ce:

“Mun shigo APC ne saboda mun gamsu da jagoranci mai kyau da gwamnan mu ke yi, cigaban da jihar mu ta yi wanda kowa ke kallo da idonsa da kuma yadda ya jajirce wajen shawo kan tattalin arzikin jiha lokacin Annoba.”

Kun zama ɗaya da kowa – APC

A jawabinsa, ɗan takarar mataimakin gwamna na APC, Sanata Umar Tafida, ya yaba da matakin masu sauya sheƙan duba da cigaban da jam’iyya ta kawo a matakai uku na mulkin ƙasar nan.

Haka nan, shugaban APC a ƙaramar hukumar Maiyama, Alhaji Saidu Giwa-Tazo, ya tabbatar musu da cewa ba za’a nuna musu banbanci ba, sun zama yan gida ɗaya da sauran mambobi.

Ya kuma bayyana tsantsar jin daɗinsa ganin cewa jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Maiyama ta ƙara ƙarfi fiye da lokacin baya.

Daga cikin manyan jiga-jigan da suka halarci gangamin sun haɗa da mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kebbi, Alhaji Usman Ankwai, kwamishinoni da hadiman gwamna.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here