Yajin Aikin ASUU: KASU ta yi Biris da Umarnin Gwamna El-Rufai

 

Malamai a Jami’ar Jihar Kaduna wato KASU, mambobi na kungiyar ASUU sun ki komawa bakin aiki duk da barazanar kora da Gwamna El-Rufai ya yi.

Malaman, cikin wani sanarwar bayan taro mai dauke da sa hannun shugaban ASUU da sakatare na jami’ar sun ce ba su yi wa daliban jarrabawa ba don har yanzu ba dage yajin aiki ba.

Sun ce akwai matsaloli tattare da jarrabawar, kuma za su tattara bayanai su tura wa hukumar kula da jami’o’i kana za su hukunta malaman da suka yi wa dalibai jarrabawar.

Kaduna- Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya, ASUU, reshen Jami’ar Kaduna (KASU) ta ki komawa aji duk da barazanar da Gwamna Nasir El-Rufai ya yi na cewa zai kore su.

Mahukunta a makaranatar sun bukaci dalibai su dawo aji domin su cigaba da jarrabawansu bayan barazanar da gwamnan ya yi.

A ranar Litinin, an ga wasu daliban a aji suna rubuta jarrabawa inda shugaban jami’ar da wasu malamai ke duba su.

Daily Trust ta gano cewa mambobin ASUU ba su shiga cikin wadanda ke duba daliban da ke rubuta jarrabawar ba suna ikirarin cewa har yanzu suna yajin aiki.

Kungiyar, a karshen wani taro da ta yi a Jami’ar ta Kaduna a ranar Litinin ta ce akwai matsaloli tare da jarrabawar.

Shugaban ASUU na jami’ar ta KASU, Kwamared Peter Adamu, da sakatarenta Kwamared Usman Abbas ne suka saka hannu a sanarwar.

Sanarwar ta ce:

“Kungiyar za ta tattara dukkan matsalolin da ta lura da shi a yayin jarrabawar da aka yi ta tura wa hukumar kula da jami’o’i na kasa.

“Mambobin ASUU na KASU ba su yi wani jarrabawa ba domin yajin aikin da ake yi har yanzu kuma ba za su gajiya ba.

“Ana lura da dukkan saba dokoki da mambobin suka yi kuma za a hukunta su bisa dokokin kungiyar a lokacin da ya dace,” in ji shi.

Martanin Shugaban KASU

A bangarensa, Shugaban Jami’ar ta KASU Farfesa Abdullahi Ashafa, ya ce a makarantarsu, KASU-ASUU ta shiga yajin aikin ne don kara ga jami’o’in tarayya amma matsalolin da ake yajin aikin saboda su ba su shafe su ba.

“Don haka ya kamata mu zama masu kishin kasa, daliban mu sun zauna gida fiye da watanni biyar kuma babu alamar za a warware matsalar.

“Jiya, an kara tsawaita yajin aikin da makonni hudu, amma abin da ASUU ke nema wurin gwamnatin tarayya bai shafe mu ba,” in ji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here