Matar da ta Nemi Mijin Wata, Ko Mijin da ya Nemi Matar Wani ba Laifi Bane a Ghana – Malamin Jami’a

 

Malamin jami’a a kasar Ghana ya bayyana cewa, ba laifi bane a kasar idan aka kama mutum da matar wani.

Ya sanar da cewa, a tanadin dokar kasar, babu hukuncin mai neman matar wani ko mace da ta nemi mijin wata.

A cewarsa, dalibansa sun shiga matukar mamaki yayin da yake bayyana musu hakan, sai dai yace rashin da’a ne da cin amana.

Wani malamin jami’a ‘dan asalin kasar Ghana yana cewa idan mace ko namiji ta/ya kwanta da mijin wata ko matar wani, hakan ba laifi bane a kasar.

Yace cin amanar aure a kasar ba laifi bane kawai dai rashin da’a ne, hakan yasa babu mai iya kai mutum gidan yari bayan an kama shi da miji ko matar wani.

Malamin makarantar wanda aka zanta da shi a Ghana BFS, yace lokacin da yayi wa daliban sa maganar hakan sun bayyana mamakinsu.

Malamin makarantar yace babu wanda zai iya kai karar kwarton matarsa ga ‘yan sanda balle a kama shi ko a kai shi kotu.

Ya kara da bayanin cewa, akwai hukuncin saki amma har yanzu ba a riga an ayyana shi da laifi bane a jihar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here