Mahamady Doumbouya: Abubuwa Game da Sojan da ya Jagoranci ƙwace Mulki a Guinea
Wani juyin mulkin soja a kasar Guinea ya kawo karshen mulkin Shugaba Alpha Conde mai cike da ce-ce -ku-ce, kasa da shekara guda bayan da ya lashe zabe a wa’adi na uku wanda ya yi sanadiyyar haifar da mummunanr zanga -zanga da zubar da jini a kasar ta Yammacin Afirka.
Dakarun runduna ta musamman a kasar da ake kira (GFS) ne suka tsare Conde, mai shekaru 83, a ranar 5 ga Satumba, sa’o’i bayan da aka samu rahoton harbe -harbe a kusa da fadar shugaban kasa a Conakry.
Kwamandan GFS Kanar Mahamady Doumbouya ya tabbatar da karbe mulkin a gidan Talabijin na kasar kuma ya yi alkawarin sa ido kan sauyi cikin lumana.
Kanal Doumbouya, wanda rahotanni suka ce ya samu horon sojoji mai yawa a Faransa, ga dukkan alamu shi ne jagoran tawagar juyin mulkin da aka yi wa lakabi da National Rally and Development Committee (CNRD).
Kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta Yammacin Afirka Ecowas, da Kungiyar Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya sun yi Allah wadai da juyin mulkin kuma ana sa ran za su matsa lamba ga gwamnatin mai ci ta mika mulki ga gwamnatin rikon kwarya ta farar hula.
Da alama jagororin juyin mulkin sun samu kwarin gwiwa ne daga ganin irin yadda hakan ta faru a makwabtan Guinea, wato Mali da kuma Chadi, kuma ana danganta hakan da raunin martani ga irin wannan lamari a wadannan kasashe.
Babban abin da ya kamata ku sani
Babu wasu cikakkun bayanai game da farkon rayuwar Doumbouya, sai dai shi ma dan kabilar Malinke ne kamar Shugaba Conde kuma ya fito ne daga Yankin Kankan na Gabashin Guinea.
Ya taba zama a Forecariah da ke yammacin Guinea, inda ya yi aiki a ƙarƙashin ofishin kula da yankuna (DST) da kuma ayyukan leken asiri gaba ɗaya.
An rawaito Doumbouya ya halarci Kwalejin Horar da dabarun yaki a birnin Paris da ke Faransa. Yana da kwarewar aikin soja na shekaru 15, ciki har da halartar yaki a Afghanistan, da Cote d’Ivoire, da Djibouti da Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya da Isra’ila, da Cyprus da Birtaniya da Guinea Bissau.
An ce Kanal din jan gwarzo ne a aikin sojoji, domin ya kammala dukkan wadannan ayyuka cikin nasara da kwarewa.
A zamansa a Isra’ila da Senegal ya kara halartar kwalejojin horar da siddabarun yaki inda ya samu shaidar laƙantar harkar tsaro a can.
Ya yi aiki a matsayin wailin gwarazan sojojin Guinea a Faransa har zuwa 2018 lokacin da shugaba Conde ya nemi ya koma gida don jagorantar babbar rundunar GFS, wadda aka kafa a bara.
Jayayya
Tun daga shekarar 2018, an samu rahotanni da dama a kafafen yada labarai na Guinea da ke sanya shakku kan cancantar Doumbouya.
Read Also:
A watan Oktoban 2018, Le Guepard ya gargadi ‘yan Guinea game da yiwuwar fadawarsu cikin wata sabuwar rayuwa da shi Dambouya zai zamar musu kadangaren bakin tulu.
A watan Agusta na 2021, Friaguinee ta yi zargin cewa an hana Dombouya zama ɗan Faransa saboda “ana ganin halayensa sun saɓa wa ƙima da ƙa’idodi” na rundunar sojojin Faransa.
Yayin da take ba da rahoto kan kadarori da dama da ake zargin mallakar kanal ne, Friaguinee ta nuna: “Ta yaya wannan jami’in, wanda ke karɓar albashi na wata-wata na kasa da Dala 500 zai iya mallakar wadannan kadarori.
A watan Mayu, Doumbouya na daga cikin jami’ai 25 na Guinea da aka ware wa takunkumin da EU ta saka saboda take hakkin dan adam, an ma yada jita-jitar cewa an tsare shi a Camp Dubreka a yammacin Guinea amma daga baya aka sake shi.
Abin da aka ji ya fito daga bakinsa
“Halin zamantakewa da siyasa da tattalin arziƙin ƙasar, da tabarbarewar cibiyoyin gwamnati da karkatar da tsarin shari’a, da keta haƙƙin ‘yan ƙasa, da rashin girmama ƙa’idodin dimokiraɗiyya, da wuce gona da iri da almundahana a bangaren kudin kasar da talauci da cin hanci da rashawa da ya zama ruwan dare ne ya sa sojojin wannan kasa suka sauke nauyin da ke kansu ga mutanen Guinea a wannan rana” in ji Dambouya.
“Dole ne mu taimaki mutanen Guinea su fita daga wannan halin saboda muna buƙatar hakan. Muna roƙon dukkan sojoji su ci gaba da zama a barikinsu kuma su ci gaba da ayyukansa na yau da kullun, wanda ya haɗa da tsaron iyakoki,” a cewarsa.
Ya ƙara da cewa “Manufar mu ita ce tabbatar da cewa jama’ar Guinea sun kasance masu haɗin kai kuma suna cin moriyar fa’idodin wannan ƙasa. Ba mu zo wasa da gwamnati ba. Za mu koyi darasi daga dukkan kura-kuran da aka yi a baya.”
Abin da wasu ke faɗi
“Wannan cukumurɗa sai ta tuna min da faretin sojojin da aka yi a filin wasa na Guinea a ranar 28 ga Satumba, inda muka ji cewa Shugaba Alpha Conde da sauran ‘yan Guinea na alfahari da wannan runduna ta musamman. Amma abun da basu sani ba shi ne ɗan zaki muka kiwata, yanzu ga shi ya zo ya gama da mu.” in ji mai kamfanin wata jarida mai zaman kanta da ake kira Espace.
“Wannan mutumin bai da horon sojoji wanda zai ba shi damar zama sojan mai saukin kai a wanan zamanin da ake ciki. Shi ya sa ma cikin shekaru biyar da ya yi a kasashen waje kamar Faransa ko mukamim Kofur bai taba wucewa ba… daga ji kuwa an ce Kofur ya zama shugaban kasa kasan lallau akwai babbar matsaka ba ƙanƙanuwa ba,” in ji mutumin.
Tambayar da dole ne ‘yan kasar Guinea su yi wa kansu ita ce, shin anya mutumin da aka kora daga rundunar sojojin Faransa saboda rashin ɗa’a na da dattakun da ya dace da shugabanci?