Tsohon Minista Lokacin Mulkin IBB, Anthony Ukpo ya Mutu

 

Tsohon Ministan Yada Labarai a lokacin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida kuma daga baya ya zama Shugaban Soja na Jahar Ribas, Birgediya Janar Anthony Ukpo mai ritaya ya rasu.

Birgediya Janar Anthony Ukpo ya rasu da safiyar Litinin 6 ga watan Satumba.

Lauyan tsarin mulki, Leonard Anyogu, sakataren kwamitin kirkirar jahar Ogoja wanda Ukpo ke jagoranta, ya tabbatar da mutuwar tsohon shugaban sojojin.

A makon da ya gabata, biyu daga cikin manyan ‘yan uwansa sun mutu.

Madam Lydia Ukpo ta mutu a Amurka, yayin da Archbishop Joseph Edra Ukpo shima ya mutu.

Anyogu ya bayyana cewa Ukpo ya mutu da sanyin safiyar Litinin a wani asibiti.

Ya ce Ukpo ya mutu sakamakon ciwon da ya dade yana fama dashi.

Ya ce:

“Zan iya tabbatar da cewa tsohon shugaban sojojin ya mutu da safiyar yau. Ya rasu a asibiti a safiyar yau.

Karin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here