Jahohin Arewa da Kudanci Kasar Nan da Suka fi Cin Moriyar Harajin VAT

 

Alkaluma sun nuna Legas ce jahar da ta fi kowace cin moriyar harajin VAT.

Kano, Kaduna, Katsina suna cikin jahohin da suke tashi da kaso mafi tsoka.

Jahohin Nasarawa da Bayelsa sun samu 10% na abin da aka ba jahar Legas.

Nigeria – Jahohin Arewacin Najeriya biyar da wasu biyar daga kudancin Najeriya sun karbi N373.84bn daga cikin N836.51bn da aka samu daga VAT.

Jaridar Punch tace wadannan jahohi goma sun karbi wadannan kudi ne a cikin watanni 14.

Binciken da hukumar tattara alkaluma na kasa watau NBS ta fitar a game da kason FAAC ya bayyana abin da aka ba jahohi tsakanin farkon 2020 da 2021.

Jahohin da ke gaba a cin VAT

Jahohin da ke kan gaba wajen samun kudi daga harajin VAT a wannan lokacin su ne:

1. Lagos (N153.94bn)

2. Kano (N32.48bn)

3. Oyo (N29.85bn)

4. Rivers (N28.43bn)

5. Kaduna (N24.75bn)

6. Katsina (N22.72bn)

7. Delta (N20.91bn)

8. Bauchi (N20.49bn)

9. Anambra (N20.14bn)

10. Jigawa (N20.13bn).

Gwamnonin da ke yankin Kudu maso yamma sun samu N256.21bn, sai na Arewa maso yamma suka tashi da N154.41bn, na Kudu maso kudu sun ci N119.88bn.

Rahoton yace jahohin Arewa maso gabas sun samu N107.43bn, na Arewa maso tsakiya sun karbi N106.58bn. Abin da kudu maso gabas suka ci shi ne N91.99bn.

Su wanene jahohin da ba su samun kaso mai tsoka?

Jahohin da ba su samun wasu kaso mai tsoka daga abin da aka tattara a asusun VAT su ne:

1. Nasarawa (N15.36bn)

2. Bayelsa (N15.79bn)

3. Taraba (N16.23bn)

4. Gombe (N16.33bn)

5. Kwara (N16.35bn)

6. Ekiti (N16.46bn)

7. Yobe (N16.90bn)

8. Abia (N17.03bn)

9. Ebonyi (N17.04bn)

10. Cross River (N17.17bn).

Gwamnatin tarayya na raba abin da aka tara a asusun harajin VAT ta hanyar la’akari da adadin mutanen da ke jaha, abin da aka samu a jaha da kuma daidaito.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here