Jam’iyar PDP ta Dakatar da Ayyukan Siyasa da Shirin Zabe Saboda #EndSars
PDP ta dakatar da duk wasu ayyukan siyasa da na jam’iyya sakamakon kashe-kashen matasa dalilin zanga-zangar EndSARS
Read Also:
A cewar Sakataren yada labarai na jam’iyyar, Kola Ologhondiyan, wajibi ne su dakatar da komai saboda tashin hankalin da Najeriya take ciki – A cewarsa, sun roki INEC da ta taimaka ta matsar da zaben da za’ayi ranar 31 ga watan Oktoba zuwa lokacin da aka samu zaman lafiya Jam’iyyar PDP ta ce ta dakatar da duk wasu ayyukan siyasa a yanzu. Jam’iyyar ta sanar da hakan ne a wata takarda da sakataren yada labaran jam’iyyar, Kola Ologbondiyan, ya saki a ranar Juma’a a Abuja. Ologbondiyan ya ce sun dauki wannan matakin ne don nuna alhininsu a kan kisan matasa da aka yi a Lekki Toll Gate da sauran kashe-kashe da aka yi sakamakon zanga-zangar EndSARS.
Dama da safiyar Alhamis jam’iyyar PDP ta umarci a kwantar da tutocin ta da ke kowanne ofishi a fadin kasar nan saboda lokacin nan mai cike da kalubale. PDP ta roki INEC ta dage zabuka 15 da aka shirya yi a ranar 31 ga watan Oktoba a kasar nan.
NAN ta sanar da cewa, a ranar Laraba, INEC ta sanar da dage zabukan sanatoci 6 da kuma na mazabu 9 a jihohi 11. INEC ta ce za ta cigaba da duban yanayin lafiyar kasa da kwanciyar hankali don samar da lokacin da za’a yi zabukan cikin sati 2. PDP ta yi kira ga ‘yan Najeriya, da su kwantar da hankulan su, kuma su cigaba da addu’a har mafita ta samu, don tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiya.