Jami’an Tsaro na Kallo Mutane Suka Sace Tallafin COVID-19 a Kwara

Wani abun al’ajabi ya faru a ranar Juma’a, inda dandazon mutane suka balle babban dakin ajiyar kaya, suka kwashe kayan tallafin COVID-19

Babban abun mamakin shine, yadda mutanen suka yi warwason kayan a gaban jami’an tsaro, ba tare da sun tanka masu ba – Sai dai, gwamnatin jihar Kwara, jihar da lamarin ya faru, ta yi Allah wadai da wannan mummunar dabi’a ta satar ‘kayan da ba naka ba’

A ranar Juma’a, wasu dandazon jama’a suka balle wani babban dakin ajiya, inda suka kwashe kayan tallafin annobar, kamar yadda Channels TV ta ruwaito. An boye kayan ne a babbar tashar jirgin sama na kasa da kasa da ya ke Ilorin, jihar Kwana, a bangaren ajiye kayayyaki na manyan jirage. Mutanen sun balle kofar shiga bangaren inda suka bude babban dakin ajiyar kayan tallafin da tsakiyar rana, yayin da jami’an tsaro ke kallonsu, ba tare da yin wani abu ba.

gest posting agency

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here