Zaben Maye Gurbi:Jam’iyyar da ta Lashe a Zamfara
Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben da aka karasa na dan majalisa mai wakiltan mazabar Bakura a jihar Zamfara ya lashe zabe.
Hukumar INEC ce ta kaddamar da Ibrahim Tudu a matsayin wanda yayi nasara bayan ya samu kuri’u 23,874.
Babban abokin hamayyarsa na APC, Dan Kande Bello ya samu kuri’u 16,546.
Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da Ibrahim Tudu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin wanda ya lashe zaben da aka sake na mazabar Bakura a jihar Zamfara.
Baturen zaben, Yahaya Tanko na jami’ar Usmanu Danfodio, Sokoto, ya ce Mista Tudu ya lashe zaben da kuri’u 23,874.
Read Also:
“Dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Mista Dan Kande Bello, ya samu kuri’u 16,546, yayinda Mista Ibrahim Tudu na PDP ya samu kuri’u 23,874 sannan an kaddamar da shi a matsayin wanda aka zaba,” in ji shi.
Shugaban PDP a jihar, Tukur Dan-Fulani, ya zanta da manema labarai jim kadan bayan sanar da sakamakon.
Ya bukaci wanda yayi nasara da ya tabbatar da nasararsa ta hanyar zama jakadan jam’iyyar na gari, jaridar Premium Times ta ruwaito.
A ranar Talata ne APC ta sanar da cewar za ta kauracewa zaben.
Mista Ibrahim Birnin-Magaji, sakataren labaran jam’iyyar a jihar, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta janye ne saboda bata da karfin gwiwa a kan INEC da hukumomin tsaro a jihar.