Jamb ta Soke Tsarin ƙayyade Makin Jarabawar da Zai ba ɗalibai Damar Shiga Makarantun
Hukumar Jamb da ke shirya jarrabawar shiga Jami’o’i da sauran makarantun gaba da sakandare a Najeriya ta sanar da soke tsarinta na ƙayyade makin jarabawar da zai ba ɗalibai damar shiga makarantun.
Hukumar wacce ta sanar da ɗaukar matakin a ranar Talata a wani taron kwamitin gudanarwarta, ta ce yanzu makarantu ne ke da ƴancin ƙayyade makin da suke buƙata a jarabawar Jamb ga ɗalibai.
Read Also:
Shugaban hukumar ta Jamb Farfesa Ishaq Oloyede, yayin bayyana matakin a taron na masu ruwa da tsaki, ya ce wasu jami’o’i sun gabatar da makin da suka ƙayyade.
A wajen taron a cewarsa, Jami’ar Maiduguri ta gabatar da maki 150. Jami’ar Usman Danfodio da ke Sokoto ta gabatar da maki 140. Jami’ar Bayero ta gabatar da maki 180 a matsayin wanda ta ƙayyade.
Taron na masu ruwa da tsaki ya kuma amince da ranar 29 ga Oktoban 2021, a matsayin wa’adin kammala sauya tsarin na ɗaukar sabbin ɗalibai a shekarar 2021.