Bayan Kai Hari: Sojoji Sun Fatattaki Mayakan ISWAP Daga Rann Dake Borno

 

Zaman lafiya ya dawo Rann, jama’a sun koma harkokin su bayan sojoji sun yi nasarar fatattakar miyagun ‘yan ISWAP.

Kamar yadda masana wurin suka kimanta, a kalla daga Rann zuwa Maiduguri, babban birnin jahar Borno ya kai tazarar 350km .

Majiyoyi masu karfi sun tabbatar da cewa mayakan ISWAP din sun isa wurin da yawan su suna harbe-harbe.

Rann, Borno – Mayakan ISWAP sun kai wa sansanin sojoji da ke Rann farmaki, hedkwatar aiwatar da mulkin karamar hukumar Kala-Balge ta jahar Borno.

Tazarar Rann zuwa Maiduguri, babban birnin jahar Borno ya kai 350km.

Majiya masu karfi sun sanar da Daily Nigerian cewa mayakan ISWAP sun isa garin ne da yawansu inda suka yi ta harbe-harbe.

Wasu mazauna yankin, musamman fararen hula sun yi ta tsere zuwa dazuka yayin da ma’aikatan jin kai suka yi ta tserewa wuraren Kamaru.

Sai dai labaran da suka riski Daily Nigerian sun tabbatar da cewa tun bayan farmakin komai ya dawo daidai a yankin.

Wasu mazauna yankin da aka tattauna dasu a safiyar Talata sun ce yawancin mazauna yankin sun koma gidajen su bayan sojojin kasa da na sama sun yi gaggawar kawo dauki.

An tattaro bayanai a kan yadda zaman lafiya ya dawo yankin tun bayan shugaban wata runduna, Christopher Musa ya bai wa rundunar soji umarnin gaggawar zuwa wurin don kwantar da tarzomar da kuma fatattakar ‘yan ta’addan.

An samu bayani a kan yadda rundunar wacce mai rikon kwaryar GOC na yanki na 7, Abdulwahab Eyitayo ya jagoranta suka yi ta ragargazar ‘yan ta’addan. Wata musayar wuta ta auku tsakanin rundunar sojoji da wasu ‘yan ta’adda wacce ta kwashe sa’o’i ana yi.

Daga nan ‘yan ta’addan suka samu suka sulale daga sansanin sojojin.

Sai dai sun ragargazu bayan sojojin sun bude musu wuta wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan ‘yan ta’addan da dama sannan wasun su suka tsere da miyagun raunuka,” kamar yadda wani jami’in binciken sirri ya sanar da The Nation.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here