Manyan ‘Yan PDP 3 da Ake Ganin Zasu Tsaya Takarar Shugaban Kasa a 2023

‘Yan siyasa a fadin kasar na gwagwarmayar ganin sun cimma nasara gabannin zaben 2023.

Akwai wasu manyan ‘yan siyasa da ake ganin za su sake tsayawa takarar neman tikitin shugaban kasa na PDP.

Wadannan ‘yan siyasa sune Bukola saraki, Atiku Abubakar da kuma Aminu Tambuwal.

Yayin da zaben shugaban kasa na 2023 ke karatowa, ‘yan siyasa a fadin jam’iyyun siyasa sun fara hararar tikitin jam’iyyarsu domin zama yan takara.

Ga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), akwai ikirarin cewa manyan sunaye za su sake fitowa kamar yadda aka yi a zaben 2019.

Wasu daga cikin manyan jiga-jigan da ake sa ran za su fafata don neman tikitin takarar shugaban kasa na PDP su ne Bukola Saraki, Atiku Abubakar, da Aminu Tambuwal, duk da cewa har yanzu ba su nuna sha’awarsu a takarar ba.

1. Atiku Abubakar

Tare da gogewarsa sosai a harkar jagoranci, da alama Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa, zai yi iya bakin kokarinsa don ganin ya dare kujerar mulki a 2023.

A zahirin gaskiya, akwai tsammanin haka musamman tsakanin magoya bayan Atiku na arewacin kasar, wanda kwanan nan daya daga cikinsu ya shaidawa Vanguard cewa dattijon dan siyasar zai fito takarar shugaban kasa ne saboda muradun ‘yan Najeriya.

Sai dai wata kungiya mai suna People’s Democratic Party (PDP) Action 2023 ta gargadi Atiku da kada ya tsaya takarar kujerar, bisa zargin cewa ya yi watsi da jam’iyyar adawa, jaridar Daily Trust ta rawaito.

2. Aminu Tambuwal

Kasancewar ya tara abokai da yawa a fadin tarayyar kasar, gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya kasance tawaga mai karfi da za a sanya idanu a kansa gabannin zaben.

Tambuwal na daya daga cikin wadanda ke more kyakkyawar alaka da tsohon shugaban sojojin Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

3. Bukola Saraki

2023 ba zai zama karon farko da tsohon shugaban majalisar dattawa zai bayyana burinsa na zama shugaban Najeriya ba.

Saraki, wanda a cikin tarihin siyasarsa ya rike mukamin gwamnan jahar Kwara, ya shiga wani rukuni na siyasa a Najeriya.

Wani memba a kwamitin NEC na PDP ya yi magana a kanshi cewa:

“Saraki zai yi yaki da sauran mutane bisa la’akari da goyon bayan da ya samu zuwa yanzu daga tuntubarsa na kasa baki daya. Zai yi takara.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here