Malamin Kwaleji ya Shigar da Karar Daliban da Sukai Masa Askin Dole a Jahar Jigawa

 

Wasu dalibai 10 sun kutsa gidan wani mutum cikin dare sun masa askin dole a Jigawa.

Rundunar yan sanda ta ce ta yi nasarar kama shida cikin daliban 10 bayan mutumin ya yi korafi.

Kakakin yan sandan Jahar Jigawa, ASP Shiisu ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin gaban kotu idan an gama bincike.

Rundunar yan sanda a Jahar Jigawa ta kama wasu dalibai shida da suka kutsa gidan wani mutum suka aske masa gashin kansa karfi da yaji, News Wire NGR ta rawaito.

Ana kan neman wasu karin mutane hudu da ake zargin yayin da tuni yan sandan sun bazama nemansu don kama su.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jigawa, ASP Lawan Shiisu, ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai da ya yi a Dutse a ranar Talata kamar yadda News Wire NGR ta rawaito.

A cewar Shiisu, sun kutsa gidan wanda abin ya faru da shi a ranar 20 ga watan Agusta misalin karfe 1 na dare.

Wanda abin ya faru da shi mai suna Ibrahim Sambo mazaunin unguwar Yalwawa Quaters a Dutse ya kai korafi ofishin yan sanda a ranar 27 ga watan Agusta.

An ce daliban suna karatu ne a ‘Jami’ar Tarayya ta Dutse da Kwalejin Fasaha ta Jigawa, Dutse.’

Kakakin yan sandan ya ce wanda ya shigar da korafin ya kuma ce ya fara rashin lafiya kwanaki biyu bayan afkuwar lamarin.

Shiisu ya ce:

“A ranar 27 ga watan Agusta misalin karfe 4 na yamma, wani Ibrahim Sambo mazaunin Yalwawa Quaters, Dutse, ya yi korafin cewa a ranar 20 ga watan Agusta misalin karfe 1 na dare, wasu daliban Jami’ar Tarayya ta Dutse da Jigawa Polyteknik, Dutse, sun kutsa gidansa, sun daure shi suka yi masa aski na dole suka tafi.

“Bayan kwanaki biyu ya fara rashin lafiya.”

An yi nasarar kama shida cikin daliban

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here