Jamus ta yi Kira a Gudanar da Bincike Akan China Kan ɗaure Musulmin Uighur
Jamus ta yi kira a gudanar da bincike na keke da keke game da zarge-zargen cewa China ta kirkiri wani tsarin garkame mutane a wani sansani da gidajen yari domin ɗaure musulmin kabilar Uighur, da kuma wasu kabilu marassa rinjaye na yankin Asiya.
Read Also:
Ministar harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock,ta kira takwaranta na China don su tattauna kan samar da sabbin hujjoji kan batun take hakkin dan adam a yankin Xinjiang.
Jewher Ilham, wata mai rajin kare hakkin ‘yan kabilar Uighur, wadda kuma aka daure mahaifinta tun shekarar 2014 ta ce tana maraba da wannan mataki na Jamus.
Tuni sakataren harkokin wajen Birtaniya Liz Truss, ya kira zarge-zargen a matsayin abin kaduwa.
Wasu bayanai da akayi kutse aka dauko daga kwamfutocin gwamnatin China sun nuna cewa an tanadi hukuncin ɗauri ga duk wani da ya nuna alamar zama musulmi.