Kotu ta Jaddada Shehu Sagagi a Matsayin Shugaban Jam’iyyar PDP na Kano

Wata kotu da ke zama a jihar Kano ta tarayya a ranar Talata ta jaddada Shehu Sagagi a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na Kano.

Shehu Sagagi, wanda na hannun daman Kwankwaso ne, an dakatar da shi daga ayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar PDP.

Kotun ta ce Bello Bichi, wanda ya shigar da karar bashi da hurumin hakan saboda bai kasance mamba na shugabannin jam’iyyar ba.

Kano- Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Kano a ranar Talata ta janye umarninta na hana shugaban jam’iyyar PDP, Shehu Sagagi daga bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar na jihar.

Ana zargin Sagagi na hannun dama ne ga gwamnan Kano kuma dan takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar NNPP, Daily Nigerian ta rawaito.

A ranar 17 ga watan Mayu, Alkali A.M Liman ya bayar da umarnin wucin gadi na dakatar da shugabannin jam’iyya karkashin shugabancin Sagagi a Kano daga amfani da wani karfin iko har sai an kammala jin karar.

Bello Bichi ne ya shigar da karar hukumar zabe mai zaman kanta, PDP da wasu mutum 40.

A yayin janye umarnin a ranar Talata, Alkali Liman ya ce mai kara, Bello Bichi, ya kautar da kotu inda ta yarda da cewa akwai bukatar gaggawa kan lamarin.

Ya kara da cewa, Bichi ba shi da karfin shigar da karar saboda bai bayyana wata shaida cewa shi mamba na kwamitin shugabannin jam’iyyar.

Alkali Liman ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Mayu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here