Muhammad Jibrin Dan Barde ya Lashe Tikitin Takarar Gwamna a Jahar Gombe

Jihar Gombe – Muhammad Jibrin Dan Barde ya lashe tikitin takarar gwamna a jam’iyyar PDP a zaben 2023 a jihar Gombe da aka gudanar.

Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, jami’in zabe, Mista Mike Oghiadomhe, ya ce Barde, ya samu kuri’u 160 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Dr Jamilu Isyaku Gwamna, wanda ya samu kuri’u 119.

Sauran ‘yan takarar, sun hada da AVM Adamu Shehu Usman (rtd) ya samu kurih’u 18, Dakta Abubakar Ali Gombe, da kuri’u 17, Dakta Babayo Ardo Kumo ya samu kuri’u 13, yayin da Dokta Gimba Ya’u Kumo ya samu kuri’u daya tilo.

Dan Barde shi ne wanda ya kafa kuma tsohon manajan darakta kuma babban jami’in bankin Sun Trust, inji rahoton Daily Trust.

Shi ne wanda ya zo na biyu a zaben fidda gwani na gwamna a 2018 wanda ya samar da gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben 2019.

A wani takaitaccen jawabi, Barde ya bayyana sakamakon a matsayin nasara ga ‘ya’yan jam’iyyar PDP a jihar.

Ya kara da cewa lokaci ya yi da za a kori gwamnatin APC a jihar.

Karin bayani na nan tafe…

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here