Shugaba Buhari ya yi Allah Wadai da Kisan Rashin Imani da Ake Yiwa Bayin Allah a Yankin Kudu Maso Gabas

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kakkausar martani bayan kisan wata yar arewa da yayanta hudu a jihar Anambra.

Buhari ya sha alwashin daukar tsatsauran mataki a kan yan awaren IPOB da ke yiwa mutane kisan rashin tausayi a yankin kudu maso gabas.

Ya kuma gargadi ’yan Najeriya da su guji gaggawar yanke hukunci ko daukar duk wani matakin da zai dada dagula al’amura, inda ya nemi a kyale doka ta yi aikinta.

Abuja- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan rashin imani da ake yiwa bayin Allah da basu ji ba basu gani ba a yankin kudu maso gabas da sauran yankunan kasar.

Shugaban kasar, a cikin wata sanarwa daga kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya gargadi masu aikata ta’asar da su tsammaci mataki mai tsauri daga rundunonin tsaro, Daily Trust ta rahoto.

Fadar shugaban kasar ta kuma yi gargadi kan daukar kowanne irin mataki na ramuwar gayya daga kowane bangare na kasar.

Ya kuma bayyana cewa jami’an tsaro na gudanar da bincike kan sahihanci da gaskiyar hotuna masu tayar da hankali da ake yadawa a kan kisan yar arewa da ake zaton yan awaren IPOB sun yi.

Sanarwar ta kuma yi kira ga dukkan jama’a da su guji daukan matakan gaggawa ko yanke hukuncin da ka iya kara dagula lamarin, inda ya bukace su da su bari doka ta yi aiki yadda ya kamata.

Fadar shugaban kasar ta kuma gargadi jama’a kan ci gaba da yada hotunan musamman a kafafen sada zumunta domin su ba masu yunkurin raba kan kasar kunya, sashin Hausa na BBC ta rahoto.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here