‘Yan Bindiga Sun Sace Limamin Coci Tare da Mutane 7 a Jihar Katsina

 

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wani limamin cocin katolika da wasu mutane bakwai a wani farmaki da suka kai garuruwan Katsina.

An yi garkuwa da malamin addinin, mataimakinsa da wasu bakinsu biyu a kauyen Gidan Mai Kanbu da ke karamar hukumar Kafur ta jihar.

Sannan a kauyen Bare-bari da ke karamar hukumar Safana, maharan sun yi garkuwa da mutane hudu.

Katsina- Tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da wani limamin kotolika, Stephen Ojapa Ojapa, da mataimakinsa, Oliver Okpara, a kauyen Gidan Mai Kanbu da ke karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina.

Majiyoyi a garuruwan Gozaki da Marabar Kanya sun bayyana cewa yan bindigar sun farmaki harabar cocin inda limaman cocin ke zama da safiyar yau Laraba, 25 ga watan Mayu, sannan suka yi awon gaba da shi da wasu bakinsu biyu, Daily Trust ta rahoto.

Wani mazaunin Marabar Kanya, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce yan bindigar sun zo ne a kan babura, amma sai suka faka a nesa da wajen sannan suka taka da kafa zuwa cikin cocin.

Ya ce:

“Mazauna Gidan Maikanbu sun bayyana cewa basu ji karar harbi a lokacin harin amma karar tashin babura da karfi da suka ji ya isa shaida. Bayan masu garkuwa da mutanen sun tafi ne wasu ma’aikatan cocin suka fara gudu don sanar da mutane batun harin.”

Cocin Katolika ta Sokoto ta tabbatar da sace mutanen a cikin wata sanarwa ta yanar gizo mai dauke da sa hannun Daraktan labaranta, Chris Omotosho.

Sanarwar ta ce:

“Da tsakar daren yau, 25 ga watabn Mayu, 2022, yan bindiga sun farmaki cocin St. Patrick’s Catholic Church, Gidan Maikambo, karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina.

“An sace limamin cocin da mataimakinsa Rev. Frs. Stephen Ojapa, MSP, da Oliver Okpara da wasu yara biyu a gidan.

“Babu wani bayani game da inda suke. Ku yi masu addu’an tsira da kubuta. Nagode.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here