Hukumar Kwallon Kafa ta Jamus ta Kori Kocinta, Hansi Flick

 

Hukumar kwallon kafa ta Jamus ta sallami kociyanta, Hansi Flick, bayan da Japan ta doke ƙasar da 4-1 a wasan sada zumunta.

Ya zama koci na farko da aka kora a matakin mai horar da tawagar ƙasar tun lokacin da aka ƙirƙiri aikin a 1926.

Mai shekara 58 – wanda ya ja ragamar wasa 25 tun bayan da ya maye gurbin Joachim Low a Agustan 2021 – ya yi rashin nasara a wasa huɗu daga biyar da ya buga.

An bai wa Rudi Voller aikin riƙon ƙwarya, wanda ya ja ragamar tawagar daga 2000 zuwa 2004.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com