ƙalubalantar Nasarar Tinubu: ‘Jam’iyyar LP ta Kasa Gamsar da Kotu da Hujjoji’

 

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta ce jam’iyyar LP ta kasa gamsar da kotun da hujjojin da take da su kan ƙalubalantar nasarar Bola Tinubu na APC a zaben shugaban ƙasa.

Jam’iyyar LP na zargin INEC da rage mata adadin ƙuri’u tare da ƙara wa jam’iyyar APC mai mulki a lokacin zaɓen shugaban ƙasar.

To sai dai kotun ta ce jam’iyyar ta kasa faɗin adadin ƙuri’un da ta samu kafin ta ce a rage mata, haka kuma kotun ta ce jam’iyyar ba ta bayyana sunayen rumfunan zaɓen da aka yi abain da ta yi iƙirarin.

Haka kuma LP ta yi zargin yin aringizo a zaɓen, sai dai kotun ta ce jam’iyyar ta kasa yin bayanin wuraren da aka yi aringizon ƙuri’un ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com