Sabon Farashin Mitar Wutar Lantarki

 

Gwamnatin Tarayya ta sanar da ƙarin farashin mitar wutar lantarki a duka fadin ƙasar nan.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar da ke sanya ido kan wutar lantarki ta Najeriya (NERC).

Hakan a cewar sanarwar, zai taimakawa kamfanonin damar samun isassun kuɗaɗen da za su ci gaba da kula da mitocin.

FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayyar, ta Hukumar da ke sa ido kan wutar lantarki ta Najeriya (NERC), ta sanar da ƙarin farashin mitar wutar lantarki a duka fadin ƙasar nan.

Shugaban hukumar Sanusi Garba, da kwamishinan shari’a, bada lasisi da bin doka, Dafe Akpeneye ne suka bayyana hakan a cikin wata sanarwar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sabon farashin mitar wutar lantarki

Sanarwar ta bayyana cewa mitar wutar da ake badawa a baya a kan naira 58,661.69, yanzu za ta koma naira 81,975.16, yayin da babbar wannan da ake badawa akan naira 109,684.36, yanzu za ta koma naira 143,836.10.

Ta ci gaba da cewa ƙarin farashin ya zama dole ne domin tabbatar da adalci tsakanin kamfanonin da ‘yan Najeriya masu amfani da mita.

Ta kuma ƙara da cewa hakan zai bai wa kamfanonin damar dawo da kuɗaɗen da suke kashewa wajen samar da mitar da kuma kula da ita.

A dakaci ƙarin bayani…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com