WHO ta yi Kira ga ƙasashen Duniya da su Ninka Kuɗaɗen Zuba Jari Don Kawar da Cutar Malaria
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi kira ga ƙasashen duniya ta su ninka kuɗaɗen da suke bayarwa don yaƙar cutar zazzaɓin cizon sauro don kawar da ita.
WHO ta ce kashi 96 cikin 100 na mutum 619,000 da suka mutu sakamakon cutar a shekarar 2021 a nahiyar Afirka suke.
Read Also:
A saƙon da ta aike a ranar Maleriya ta duniya, daraktar hukumar mai kula da shiyyar Afirka Dakta Matshidiso Moeti, ta ce cutar maleriya na da saurin yaɗuwa da ninki shida zuwa 20, fiye da sauran cututtuka a yankunan da cutar ta fi ƙamari.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 25 ga watan Afrilun kowacce shekara domin ƙarfafa yadda za a yaƙi cutar Maleriya a duniya.
Dakta Moeti ta ce yunƙurin da aka yi ya taimaka wajen rage adadin mutanen da ke mutuwa sakamakon cutar a nahiyar Afirka daga shekarar 2000 zuwa 2021.
Ta ce aƙalla ƙasashen Afirka 28 ne suka bayyana sha’awarsu ta fara gabatar da allurar riga-kafin cutar zazzaɓin cizon sauro d aka samar.