Jawabin Gwamnan Kano Gabannin Zanga-Zanga
Jihar Kano – Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ce gwamnati ba za ta lamunci wani yunkuri ba zai kawo tashin hankali ba a zanga-zangar da za a yi gobe Alhamis.
Abba Kabir ya faɗi haka ne a lokacin da yake jawabi ga ’yan kasuwa, sarakunan gargajiya, da malaman addini a gidan gwamnati da ke Kano yau Laraba.
Gwamna ya jaddada cewa zanga-zanga ba za ta kai mutane ko’in ba, bisahaƙa ya ja kunnen matasa su guje wa tada zaune tsaye, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Read Also:
Gwamnan Abba ya gayyaci masu zanga-zanga
“Mun samu sahihan bayanan sirri cewa wasu daiɗaikun mutane sun ɗauko hayar ƴan daba domin tada fitina a jihar Kano. Ina tabbatar muku da cewa gwamnati ba za ta lamunci haka ba.
“A maimakon haka, ina mika goron gayyata ga masu son gudanar da zanga-zanga da su zo gidan gwamnati, inda zan ji dadin sauraren koke-kokensu, sannan mu tattauna da su.”
– Abba Kabir Yusuf.
Gwamna ya ambaci wasu tsare-tsaren da gwamnatinsa ta kawo na inganta rayuwar al’umma da kuma tsamo su daga halin wahalar da ake ciki.