Gwamnatin Jigawa da Katsina Sun Saka Dokar Hana Fita
Jihar Jigawa – Gwamnatin jihar Jigawa ya sanya dokar zaman gida ta tsawon sa’o’i 24 yayin da zanga-zangar lumana ya riƙide ta zama tashin hankali ranar Alhamis.
Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi Ɗanmode ne ya sanar da ƙaƙaba dokar a wani jawabi na kai tsaye da ya yi ranar Alhamis da daddare.
A ranar farko ta zanga zangar yunwa wadda masu shiryawa suka ce ta lumana ce, an yi kashe-kashe, kone-kone da satar dukiya a jihohi da dama ciki hada Jigawa.
Read Also:
Domin daƙile yaɗuwar ɓarnar da aka yi Gwamna Umar ya sanya dokar kulle a faɗin kananan hukumomin jihar, kamar yadda Leadership ta kawo.
Gwamnan ya bayyana halin da ake ciki, a jihar a matsayin abin takaici matuka kuma ba zai zama mafita ga bukatun mutane ba.
Ita ma gwamnatin jihar Katsina ta sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a ƙaramar hukumar Dutsima, yayinda ta hana zirga-zirgar mutane daga ƙarfe bakwai na yamma zuwa ƙarfe bakwai na safe a sauran ƙananan hukumomin 33 da ke jihar.
Karin bayani na nan tafe…