Yayin Zanga-Zanga: Jihohin da Suka Saka Dokar Hana Fita
Yayin da zanga-zangar tsadar rayuwa ke ƙara ƙamari a fadin Najeriya, wasu gwamnatoci na saka dokar hana fita.
An samu rahotonnin tashin hankali da ƙone-ƙone a mafi yawan wuraren da ake yin zanga-zangar.
Read Also:
Zuwa yanzu, gwamnatin jihar Borno ta saka dokar hana fitar ne bayan “la’akari da fashewar bam da aka samu wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 16 da raunata wasu da dama a jihar,” in ji kakakin ‘yansandan jihar ASP Nahum Kenneth.
A jihar Yobe kuma, an saka dokar hana fitar ce a ƙananan hukumomi na Potiskum, da Gashua, da Nguru bayan wasu ɓata-gari sun fara lalata gine-gine da fasa shagunan mutane.
Gwamnatin Kano ma ta saka dokar a faɗin jihar tana mai cewa “domin daƙile sace-sacen kayan mutane da kuma kashe rayuka”.